Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi A farkon wannan mako mai karewa ne babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta bayyana hukunce-hukuncen da kotunan ɗaukaka ƙara suka yi, inda suka ƙwace nasarar wasu gwamnoni a matsayin "karan-tsaye" ga dimokraɗiyya. Jam'iyyar adawar na zargin APC mai mulkin Najeriya ne da "amfani da ƙarfin iko" wajen tanƙwara hukuncin kotunan, zargin da APC ta musanta. "Shari'ar Najeriya ta zama kamar rawar 'yan mata yanzu; idan an yi gaba, sai a koma baya," in ji Mataimakin Sakataren PDP na Ƙasa, Ibrahim Abdullahi. Ya ce dalilan da mutanen nan ke gabatarwa suna kwace zaben nan, akasari batutuwan da suka shafi kafin zabe ne. A cewarsa, kotun koli ta yanke hukunci da cewa: "Ba abubuwa ba ne da suka shafe ta, a hukuncin da ta bayar kan dan takararmu, Atiku Abubakar". Ya yi ikirarin cewa batun shari'ar, wata matsala da ka iya shafar ...
Comments
Post a Comment