Wolverhampton Wanderers na son aron golan Arsenal Aaron Ramsdale mai shekara 27 a watan janairu tare da neman a sayar mata da shi a kaka mai zuwa.


 Wolverhampton Wanderers na son aron golan Arsenal Aaron Ramsdale mai shekara 27 a watan janairu tare da neman a sayar mata da shi a kaka mai zuwa. (Star)



Kocin Nottingham Forest, Steve Cooper na ƙara fuskantar matsin lamba yayin da mai ƙungiyar Evangelos Marinakis ke nuna rashin jin dadi da sakamakon wasanninsu. (Mail)


Tottenham na son sayarn ɗan wasan bayan Benfca Morato sai dai ƙungiyar ba ta gaggawar da za ta sayar da ɗan wasan Brazil ɗin a watan Janairu. (Record via Sport Witness)


Damar da Newcastle ke da shi ta kashe kudi ta danganta da ko za ta rage kuɗin da take biyan ɗan wasanta na Italiya Sandro Tonali wanda aka dakatar wata 10 daga wasa saboda saba ka'idar caca. (Telegraph - subscription required)



Dan wasan Al-Hilal dan Portugal Ruben Navas ba shi ne wanda Arsenal take muradi ba, idanunta na kan ɗan Brazil dake wasa a Aston Villa Douglas Luiz a watan Janairu. (Fabrizio Romano)


Tottenham na shirin katse kwataragin golanta mai shekara 36 Hugo Lloris, wani ra'ayi da koci Ange Postecoglou ke da shi. (Football Insider)


Idanun PSG da Real Madrid da Manchester City na kan ɗan wasan Argentina da River Plate, Claudio Echeverri mai shekara 17. (Sport - in Spanish)


Chelsea da Liverpool da Manchester City na son ɗaukar matashin ɗan wasan Italiya da AC Milan Francesco Camarda wanda ya fara wasa a ranar Asabar yana da shekara 15. (90



Real Madrid ta yi watsi da damar ɗaukar dan wasan Argentina Mauro Icardi mai shekara 30 daga Galatasaray a watan Janairu. (Athletic)

Comments

Popular posts from this blog

ZARGIN 'YAN HAMAYYA KAN SHARI'0'IN KOTONA DA KOKAWAR BUHARI