Jami’an tsaro sun kama wani mutum da ke yi wa ƴan ta’adda bindigogin hannu a jigawa Fatima Abdullahi
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da ke yi wa ƴan ta’adda bindigogin hannu a jigawa
By Fatima Abdullahi November 26, 2023
<script async custom-element="amp-auto-ads"
src="https://cdn.ampproject.org/v0/amp-auto-ads-0.1.js">
</script>
Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekara 50 dake yi wa ƴan ta’adda bindigogi a karamar hukumar Ringim.
Kakakin rundunar Lawan Shiisu wanda ya sanar da haka wa manema labarai ranar Alhamis a garin Dutse ya ce jami’an tsaron sun kama mutumin ranar 16 ga Nuwamba.
“ Jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan banga sun kama wani mutum mazaunin kauyen Yandutsen Kawari dake yin bindigogi yana siyar wa mahara.
“Jami’an tsaron sun kama manyan bindigogi biyu da pistol daya a gidan mutumin.
Shiisu ya ce bayan ya shiga hannun jami’an tsaron cewa mutumin ya tabbatar cewa yana kera bindigogi sannan ya siyar wa mutane da dama da bai san adadinsu ba.
Ya ce idan rundunar ta kammala bincike za ta kai mutumin kotu domin a yanke masa hukunci.
Comments
Post a Comment