YANDA AKE YIN ORGANIC MAN ALAYYADI
Shin kina son koyon man alayyadin da baya warin da xe hanaki amfani dashi sannan kuma yayi haske kamar man zaitun? To kibiyoni don jin yadda akeyi yar uwa.
Dafarko dai xaki samu kwallon kwakwar manjan ki gwargwadon da kike bukaata, a fasa ta da kwakwar ciki xaki yi amfani, in kika sami kamar rabin kwano bararriya, ki wanketa ki shanya ta ta bushe se ki kai inji a nika miki ba ruwa xa asa miki ba wajen nikan a haka xa a nika ta, bayan kin xo gida se ki samu babbabar roba ki xuba ta aciki se ki xuba ruwa ki sa muciya ki jujjuya ta se ki barta na tsawon waso awoyi, kamar misali in da yamma ne se ki barta ta kwana.
Sannan ki dakko abun tace Kamu kitace ta kamar yanda ake yace Kamu, bayan kin ga ma seki sami leda babba kamar wacce ake sa pure water a ciki babbar ke nan se ki juye aciki in ruwan yayi yawa daya baxa ta isa ba se ki kara wata har dai ki juye shi duka, se ki ajjeyi shi na tsawon wasu awoyin, xaki ga man ya taso sama ruwan yayi kasa.
Sanna se ki huda ledan daga kasa ki tsiyaye ruwan a hankali in yazo daidai man se ki rike ledan karki bari man ya xube fa se ki sami tukun ya ki juye manki, sanna ki dorashi a wuta yar kadan xaki sa wutar bada yawaba, ki rika juyashi karki bari yakone da xarar kin ga ruwan ya gama konewa ya rage saura man se ki sauke, bayan ya sha iska se ki samu rariya ki tace man se ki kara samun wani kyallen ki sake tacewa da shi don dai kar ki bar diddiga ta shiga.
#SanaaNOBLEBLEND
Comments
Post a Comment